Ƙungiyar SERAP ta zargi ɓacewar wasu maƙudan kuɗaɗe a kamfanin mai na ƙasa (NNPCL), da suka kai Naira biliyan 825 da Dala biliyan 2.5, wanda aka ware domin gyaran matatun man fetur na ƙasar.
A wata takarda da SERAP ta fitar ɗauke da sa hannun mataimakin daraktanta, Kolawole Oluwadre, ta yi kira ga Shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari, da ya fito ya yi wa ‘yan Nijeriya bayani kan inda kuɗaɗen suka tafi.
Ƙungiyar ta ce wannan batu ya fito ne daga rahoton babban jami’in bincike na ƙasa da aka fitar a ranar 27 ga Nuwamban 2024.
SERAP ta buƙaci Mele Kyari da ya miƙa duk waɗanda aka samu da hannu wajen karkatar da kuɗaɗen ga hukumomin EFCC da ICPC don ɗaukar mataki.
Ta kuma bai wa NNPCL wa’adin kwanaki bakwai don su yi ƙarin bayani, idan ba haka ba za su fuskanci shari’a.
A halin yanzu, ‘yan Nijeriya na ci gaba da kokawa kan matsin rayuwa, musamman bayan cire tallafin mai da gwamnatin Tinubu ta yi.
Wannan ya sa cece-kuce kan ɓacewar waɗannan kuɗaɗe ya ƙara jawo hankalin al’umma.