Sakamakon kuri’un jin ra’ayin al’umma da kafar watsa labarai ta CGTN ta gudanar, ya nuna kimanin kaso 86 bisa dari na wadanda suka bayyana matsayar su sun amince cewa, cimma kyakkyawa, kuma dangantaka mai dorewa tsakanin Sin da Amurka, na da nasaba da yadda aka aiwatar da kudurorin da aka cimma daidaito a kan su, tsakanin shugabannin kasashen biyu yayin taron Bali a watan Nuwambar bara.
Idan an kwatanta sakamakon kuri’un na wannan karo da na watanni 4 da suka gabata, adadin masu rike da wannan ra’ayi a wannan lokaci ya karu da kaso 4.1 bisa dari.
- Ba Da Gudummawar Da Ta Dace Don Gina Al’umma Mai Kyakkyawar Makoma Ga Sin Da Afirka
- Firaministan Pakistan Kakar: Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Tana Girmama Bambance-bambance A Tsakanin Kasa Da Kasa
A daya bangaren kuma, kaso 91 bisa dari suna ganin cewa, ya dace bunkasar kyakkyawar alaka tsakanin Sin da Amurka ya dogara ga yadda sassan biyu ke mutunta juna, da yadda suke kallon kan su a matsayin daidai da juna. Shi ma adadin masu wannan ra’ayi ya karu da kaso 2.1 bisa dari, sama da na wanda aka samu watanni 4 da suka gabata.
Kaza lika, kaso 77 bisa dari na masu kada kuri’un sun yi kira ga kasashen biyu da su ci gaba da tattaunawa, su yi kandagarkin rashin fahimta da tafka kuskuren matsaya, kana su gaggauta ingiza alakar Sin da Amurka zuwa turba mai kyau, da daidaiton ci gaba. A ta bakin daya daga cikin su “Bude fagen shawarwari tsakanin manyan kasashe biyu wato Sin da Amurka zai haifar da manyan nasarori ga bil Adama baki daya”
Kafar CGTN ta fitar da dandalin kada kuri’un ne da harsunan Turanci, da yaren Sifaniya, da Faransanci, da Larabci da yaren Rasha, inda cikin sa’o’i 24 sama da mutane 10,000 suka kada kuri’un su.
A watannin Fabarairu, da Yuli, da Nuwamban wannan shekara, CGTN ta gabatar da dandalin kada kuri’u ta yanar gizo na kasa da kasa, game da alakar Sin da Amurka, wanda al’ummun sassan duniya daban daban har mutum 70,000 suka bayyana ra’ayoyin su. (Saminu Alhassan)