Ana ci gaba da takun saka tsakanin Burtaniya da Girka dangane da batun maido da kayayyakin tarihi na al’adu. Kwanan nan, hankalin duniya ya sake dawowa kan gidan adana kayayyakin tarihi na Burtaniya, saboda an sato yawancin kayayyakin tarihin gidan ne ta hanyar yaki da fadada mulkin mallaka na Turawa.
Sakamakon kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta yanar gizo na baya-bayan nan da CGTN ya gudanar ya nuna cewa, kashi 80.8 cikin 100 na wadanda suka kada kuri’ar sun yi imanin cewa, ajiye wadannan jerin kayayyakin tarihi na sata a gidan tarihi na Burtaniya bai dace. Kashi 90.3 cikin 100 na wadanda suka kada kuri’a suna ganin cewa, ya kamata a mayar da kayayyakin tarihi na al’adu da aka wawashe ta hanyar fadada mulkin mallaka da yaki zuwa kasarsu ta asali kuma a kan lokaci domin kaucewa ci gaba da mulkin mallaka.
Yawancin kayayyakin tarihi na al’adu dake gidan tarihi na Biritaniya suna dauke alamun sata. A tsawon shekaru, kasashe da dama da suka hada da Girka, Najeriya, Habasha, Masar, da Chile suna nema a kwato kayayyakin tarihi da aka sace daga gwamnatin Burtaniya, amma an hana su saboda abin da ake kira “kiyaye tsaron kayayyakin tarihi”. (Mai fassara: Yahaya)