Darektan cibiyar nazarin harkokin kasar Sin ta Najeriya Charles Onunaiju, ya shaidawa wakilin CMG cewa, shawarar wayewar kai ta duniya da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar, za ta haifar da alfanu ga daukacin bil Adama.
Mista Onunaiju ya fadi hakan ne a gefen taron “Demokuradiyya: Darajoji masu muhimmanci ga daukacin bil-Adama” wanda ya gudana a birnin Beijing na kasar Sin a kwanakin baya.
A cewarsa, shawarar wayewar kai ta duniya ta jaddada muhimmancin samun cudanya tsakanin al’ummu da al’adu daban daban, don tabbatar da fahimtar juna, da girmama juna, da kulawa da juna a tsakaninsu, ta yadda za a samu karin hadin kan al’ummun duniya, tare da samar da tsaro da walwala ta bai daya, wadanda za su amfani daukacin bil-Adama. (Bello Wang)