Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Chelsea na cigaba da zarce tsara a gasar Firimiya, bayan ta doke abokiyar karawarta Tottenham Hotspur da ci 4-3 a filin wasa na Tottenham Hotspur Stadium.
A mintuna goma na farkon wasan Tottenham ta zura ƙwallaye biyu ta hannun Dominic Solanke da Deja Kulusevski kafin Jadon Sancho ya farke wa Chelsea kafin tafiya hutun rabin lokaci.
- Guguwa Mai Ƙarfi Ta Sa An Soke Wasan Liverpool Da Everton Na Yau
- Leicester City Ta Kori Kocinta Bayan Rashin Nasara A Hannun Chelsea
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci Chelsea ta zura ƙwallaye uku rirgis ta hannun kyaftin ɗin tawagar Enzo Fernandez da Cole Palmer wanda ya jefa ƙwallaye biyu a bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Dab da tashi daga wasan kyaftin din Tottenham Son Heung Min ya jefa ƙwallo ɗaya, amma hakan bai hana ƙungiyar wadda koci Ange Postecoglu ke jagoranta rashin nasara ba.
Da wannan nasara da Chelsea wadda ake wa lakabi da Blues ta samu ya sa ta ɗare matsayi na biyu akan teburin gasar Firimiya da maki 31 inda Liverpool ke matsayi na ɗaya da maki 35.