Sabon mai horar da yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Enzo Maresca yana son samun sabon mai tsaron raga da zai taimakawa Robert Sánchez a sabuwar kakar wasa da za a fara a watan Agusta.
Kungiyar tana shirin kawo sabon mai tsaron raga duba da yadda take da karancin masu buga wannan wuri sakamakon Kepa Arrizabalaga dake zaman aro a Real Madrid.
Kepa zai bar kungiyar a wannan bazarar idan har Real Madrid ta saka hannu a yarjejeniyar daukarsa na din din din bayan da Andry Lunin ya yanke shawarar barin Santiago a bana.
Maresca na fatan ganin ya kai Chelsea mataki mai kyau wanda zai sa su buga gasar Zakarun Turai a badi,duk da cewar kungiyar na farfadowa daga rashin babban dan wasan bayanta Thiago Silva wanda ya bar Chelsea a karshen kakar wasar da aka kammala.