ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Waye Zai Lashe Ƙyautar Gwarzon Ɗan Wasan Afrika Na 2025?

by Abba Ibrahim Wada
10 months ago
Gwarzo

Shahararrun ‘yan wasa irin su dan wasan PSG Achraf Hakimi da Mohamed Salah na Liberpool su ne a gaba-gaba cikin jerin ‘yanwasa 10 da ake ganin za su iya lashe kyautar dan wasa mafi hazaka na Afirka na shekara ta 2025 da muke ciki.

Hakimi, mai buga bangaren dama a cikin masu tsaron baya na kungiyar Paris St-Germain da ke Faransa ya taimaka wa kungiyar wajen lashe kofin kungiyoyi na kasar da kuma gasar Zakarun Turai a kakar da ta gabata, yayin da shi kuma Salah ya lashe kyautar dan wasan da ya fi kowane zura kwallo a gasar Premier ta Ingila, yayin da kungiyar ta lashe gasar Premier ta Ingila.

  • Ƴansanda Sun Kama  Wani Mai Wasa Da Bindiga AK-47 A Cikin Wani Bidiyo A Adamawa
  • Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu

Dan wasan gaba na Eberton, Iliman Ndiaye da kuma dan wasan tsakiya na Tottenham Hotspur Pape Matar Sarr, wadanda suka taimaka wa kasarsu Senegal samun gurbin gasar cin kofin duniya ta 2026 na cikin jerin, tare kuma da dan Nijeriya Bictor Osimhen, wanda ya taba lashe kyautar a 2023.

ADVERTISEMENT

Dan wasan tsakiya na Kamaru Andre-Frank Zambo Anguissa, dan wasan gaba na DR Congo Fiston Mayele, da Denis Bouanga na Gabon, da na Guinea Serhou Guirassy da kuma dan wasan tsakiya na Morocco Oussama Lamlioui duk suna cikin jerin ‘yanwasan da aka lissafa.

Salah ya lashe kyautar a shekarar 2017 da kuma 2018, yayin da shi kuma Hakimi ya zamo na biyu a shekaru biyu da suka gabata.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

Dan wasan da ya lashe kyautar a bara, Ademola Lookman na Nijeriya ba ya cikin jerin ‘yan wasan da aka lissafo a bana, inda hukumar kwallon kafa ta Afirka (Caf) ta samar da kwamitin kwararru wanda ya zakulo masu horarwa da ‘yan wasan da suka “Taka rawar gani” a tsakanin 6 ga watan Janairu zuwa 15 ga watan Oktoban wannan shekara.

An bayyana sunan mai horar da tawagar ‘yan kwallon kafa ta kasar Cape Berde, Bubista a matsayin mai neman lashe kyautar mai horarwa mafi kwazo bayan jagorantar tawagar kasar ta Blue Sharks wajen samnun gurbin gasar kofin duniya a karon farko a tarihi.

Haka nan tawagar ta tsibirin Cape Berde na cikin masu gogayyar lashe kungiya mafi hazaka a shekarar, tare da Morocco wadda a baya-bayan nan ta lashe kofin duniya na gasar kwallon kafa ta ‘yan kasa da shekara 20.

‘Yanwasa mata na Nijeriya Esther Okoronkwo da Rasheedat Ajibade na cikin wadanda ke neman lashe kyautar zakarun ‘yanwasa mata na Afirka na wannan shekarar. Ya zuwa yanzu dai hukumar CAF ba ta bayyana ranar da za a yi bikin bayar da kyautar ba.

Dan wasa mafi Kwazo: Andre-Frank Zambo Anguissa (Napoli da Kamaru), Denis Bouanga (Los Angeles FC da Gabon), Serhou Guirassy (Borussia Dortmund da Guinea), Achraf Hakimi (Paris St-Germain da Moroko), Oussama Lamlioui (Renaissance Berkane), Fiston Mayele (Pyramids da DR Congo), Iliman Ndiaye (Eberton da Senegal), Bictor Osimhen (Galatasaray da

Nigeria), Mohamed Salah (Liberpool da Masar), Pape Matar Sarr (Tottenham Hotspur da Senegal).

Mai tsaron raga na maza: Yassine Bounou (Al Hilal da Moroko), Aymen Dahmen (CS Sfadien da Tunisia), Marc Diouf (TP Mazembe da Senegal), Edouard Mendy (Al-Ahli da Senegal), Munir Mohamedi (RS Berkane da Moroko), Stanley Nwabali (Chippa Utd da Nijeriya), Andre Onana

(Trabzonspor da Kamaru), Ahmed El Shenawy (Pyramids da Masar), Bozinha (Chabes da Cape Berde), Ronwen Williams (Mamelodi Sundowns da Afirka ta Kudu).

Mai horar da kungiyar maza: Bubista (Cape Berde), Moine Chaabani (Renaissance Berkane), Hossam Hassan (Masar), Krunoslab Jurcic (Pyramids), Mohamed Ouahbi (Moroko U20), Romuald Rakotondrabe (Madagascar), Walid Regragui (Moroko), Tarik Sektioui (Moroko U23), Pape Thiaw (Senegal), Sami Trabelsi (Tunisia).

Tawagar maza: Algeria, Cape Berde, Masar, Ghana, Ibory Coast, Moroko, Moroko U20, Senegal, Afirka ta Kudu, Tunisia. ‘Yan wasa Mata da ke takarar lashe zakarun Afirka na shekara ta 2025.

‘Yar wasa mafi kwazo: Rasheedat Ajibade (Paris St-Germain da Nijeriya), Barbra Banda (Orlando Pride da Zambia), Portia Boakye (Hapoel Petah Tikba da Ghana), Tabitha Chawinga (Lyon da Malawi), Temwa Chawinga (Kansas City da Malawi), Ghizlaine Chebbak (Al Hilal da Moroko), Mama Diop (Strasbourg da Senegal), Rachael Kundananji (Bay FC da Zambia),

Sanaa Mssoudy (AS FAR da Moroko), Esther Okoronkwo (AFC Toronto da

Nijeriya).

Mai tsaron raga na mace: Sedilame Boseja (Mamelodi Sundowns da Botswana), Andile Dlamini (Mamelodi Sundowns da Afirka ta Kudu), Habiba Emad (FC Masar da Masar), Khadija Er-Rmichi (AS FAR da Moroko), Fatoumata Karantao (MUSFAS Bamako da Mali), Cynthia Konlan (Swieki United da Ghana), Adji Ndiaye (AS Bambey da Senegal), Fideline Ndoy (TP

Mazembe da DR Congo), Chloe N’Gazi (Marseille da Algeria), Chiamaka Nnadozie (Brighton & Hobe Albion da Nijeriya).

Mai horar da kungiyar mata: Genobeba Anonman (15 de Agosto), Kim Bjorkegren (Ghana), Lamia Boumehdi (TP Mazembe), Desiree Ellis (Afirka ta Kudu), Carol Kanyemba (Zambia U17), Adelaide Koudougnon (Ibory Coast U17), Justin Madugu (Nijeriya), Bankole Olowookere (Nijeriya U17), Siaka Gigi Traore (ASEC Mimosas), Jorge Bilda (Moroko).

Tawagar mata: Kamaru U17, Ghana, Ibory Coast U17, Mali, Morocco, Nijeriya, Nijeriya U17, Afirka ta Kudu, Tanzania, Zambia U17. Za ku iya ganin cikakken jerin wadanda ke neman lashe kyautukan a shafin hukuma Caf. [1]

Gwarzo
Abba Ibrahim Wada
+ postsBio
  • Abba Ibrahim Wada
    https://hausa.leadership.ng/author/abba-ibrahim-wada/
    Yadda FIFA Ta Yi Yunƙurin Sasanta Rikicin Israila Da Amurka A Kofin Duniya
  • Abba Ibrahim Wada
    https://hausa.leadership.ng/author/abba-ibrahim-wada/
    Har Yanzu Nijeriya Tana Fatan Zuwa Kofin Duniya Na 2026
  • Abba Ibrahim Wada
    https://hausa.leadership.ng/author/abba-ibrahim-wada/
    Mece Ce Matsalar Real Madrid? 
  • Abba Ibrahim Wada
    https://hausa.leadership.ng/author/abba-ibrahim-wada/
    Ko Ka San Dalilin Da Zai Bai Wa Nijeriya Damar Zuwa Gasar Cin Kofin Duniya?

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana
Wasanni

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

September 8, 2026
Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain
Wasanni

Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain

September 7, 2026
Next Post
Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 20, Sun Ceto Mutane 17 Da Aka Yi Garkuwa Da Su

Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 20, Sun Ceto Mutane 17 Da Aka Yi Garkuwa Da Su

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.