Chelsea ta amince ta siyan golan Brighton Robert Sanchez kan kudi fan miliyan 25 da kari.
Kungiyar ta Blues ta yi ta neman kara mai tsaron gida a tawagar ta bayan sayar da Edouard Mendy ga Al-Ahli a kasar Saudiyya.
Sanchez, mai shekaru 25, zai kalubalanci Kepa Arrizabalaga a matsayin mai tsaron raga na daya
Koci Mauricio Pochettino dan kasar Sipaniya zai yanke hukunci akan wanda zai dinga tsare raga a Chelsea yayin da kocin mai tsaron gida Ben Roberts ya yi aiki tare da Raya a lokacin da yake Brighton.
Sanchez ya kasance tare da Seagulls tun yana da shekaru 15, bayan ya koma makarantar horar da yan kwallonsu su daga Levante a 2013
Bayan yin zaman aro tare da Forest Green da Rochdale, ya fara wasansa na farko na Brighton a watan Nuwamba 2020 kuma ya zama babban golan farko na Seagulls
Haka kuma kasar Sipaniya ta kira shi a shekarar 2021 kuma yana cikin tawagar ta a gasar cin kofin kasashen Turai da aka jinkirta da kuma gasar cin kofin duniya ta 2022, duk da cewa ya buga wasanni biyu kacal ga kasar Sifaniya
Sanchez ya rasa gurbinsa ne a hannun Jason Steele a gasar Premier ta Brighton ta 2022-23, duk da cewa ya buga wasan dab da na kusa da na karshe a gasar cin kofin FA a bugun fenariti da Manchester United ta yi a Wembley
Kwantiraginsa a Brighton zai kare a shekarar 2025