Hukumar yaki da maganin kara kuzari ta kasar Sin wato CHINADA ta bayar da wata sanarwa a yau cewa, ta nuna shakku ga hukuncin da aka yanke kan dan wasan tsalle-tsalle da guje-guje na kasar Amurka Erriyon Knighton dangane da shan maganin kara kuzari.
A yayin binciken da aka yi masa a ranar 26 ga watan Maris na bana, an gano alamar cewa, ya sha maganin dake kunshe steroid, amma hukumar yaki da maganin kara kuzari ta Amurka wato USADA ta tsai da kuduri na ba-zata kafin gasar da aka yi a gida ta neman samun damar shiga gasar wasannin Olympics ta Paris, ba za a hana Knighton ya shiga gasar ba saboda ya ci nama maras tsabta, kana an amince da shi ya wakilci Amurka ya shiga gasar wasannin Olympics ta Paris.
- Sin Ta Yi Kira Ga ICC Da Ta Martaba Ikon Shari’a Na Sudan
- Xi Ya Nanata Bukatar Kare Al’adu Da Kayayyakin Gargajiya Na Sin
Game da binciken maganin kara kuzari da aka yi wa ‘yan wasan kasar Sin, hukumar USADA ta nuna ma’auni biyu, ta bayar da dalilai da dama don kawar da laifin da ‘yan wasanta suka aikata, kana ta kau da kai daga bayanan hukumar yaki da maganin kara kuzari ta duniya wato WADA da kuma rahoton jami’in gabatar da kara a kotu na kasar Switzerland. Amurka ta zargi kasar Sin cewa, CHINADA da WADA sun hada hannu kan batun, ta kuma bukaci a sanya takunkumi kan ‘yan wasan kasar Sin.
Hukumar CHINADA ta yi nuni da cewa, USADA ta kau da kai daga batutuwan shan maganin kara kuzari a cikin kasar a dogon lokaci, ta bukaci a sanya takunkumi kan wasu kasashe, wannan ya shaida cewa, ta aiwatar da ayyukan bisa yunkurin siyasa da kuma nuna ma’auni biyu kan batun. (Zainab Zhang)