• English
  • Business News
Friday, October 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ci Gaban Tattalin Arzikin Kasar Sin A Watannin Farkon Bana Zai Kara Karfafa Gwiwa A Duniya

by CGTN Hausa
2 years ago
arziki

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Taya Kim Jong Un Murnar Cikar Jam’iyyar WPK Shekaru 80 Da Kafuwa

An Jinjinawa Tallafin Kamfanonin Sin Ga Tsarin Bunkasa Masana’antun Senegal

A baya-bayan nan, sassan gwamnatin kasar Sin sun fitar da alkaluma game da ma’aunan tattalin arziki 3 da suka hada da na yawan kayayyakin da masana’antu ke sayarwa, da na bangaren kasuwanci da bai shafi samar da kayayyaki ba, da kuma na samarwa da fitar da kayayyakin, wadanda suka karu da kaso 1.7 da 1.6 da 1.8 idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara.

Na tuna yadda a lokacin da gwamnatin kasar Sin ta gabatar da rahoton aiki da bayyana burinta na samun karuwar tattalin arziki da kaso 5 a bana, na ji da kunnena wasu kafafen yada labaran yammacin duniya na cewa, kasar Sin ba ta bayyana yadda za a yi ta samu wannan ci gaba ba. Wato kamar su na ganin wannan burin ba mai yuwuwa ba ne. Amma wadannan alkaluma da aka gabatar sun nuna cewa, kasar Sin ta san abun da take yi kuma ta na da yakinin cimma burikan da ta sanya a gaba. A matsayin wadda ta shafe shekaru a kasar Sin, na san kasar ba ta sanya burin da ba za ta iya cimmawa ba, ko in ce, ban ma taba ganin ta sanya wani buri da ta gagara cimmawa ba.

  • Sin Da Faransa Sun Amince Da Gina Alaka Bisa Daidaito Da Hangen Nesa 

Ci gaban da Sin ta samu cikin wadannan watanni, bai tsaya kadai ga wadannan ma’aunai 3 ba, an kuma samu bunkasar wasu manyan fannoni kamar na samar da hidimomi da rayuwar al’umma da sayyaya da sauransu. Abun da irin wadancan kafofin watsa labarai da na bayyana a baya ba su gane ba shi ne, tattalin arzikin kasar Sin na bisa tubali mai kwari dake da juriya. Haka kuma, kasar ba ta dogara da kasashen waje wajen raya tattalin arzikinta ba, domin kasar Sin ta mayar da hankali ne wajen amfani da albarkatun da ta mallaka a cikin gida da kyawawan dabarun da suka dace da ita, da kuma fasahohi da karfinta na kirkire-kirkire. Misali, a cikin bangarorin da suka samu ci gaba, akwai rayuwar al’umma da karuwar sayayya a cikin gida. Kyautatuwar rayuwar al’umma na nufin samun kwanciyar hankali da biyan bukatu da kuma samuwar wadata. Samuwar wadata kuma shi ne ke kara ingiza sayyaya da kashe kudi a cikin gida, wanda ke bayar da gudunmuwa ga tattalin arziki. A ganina, wadannan ci gaba da aka samu cikin kankanin lokaci, somin tabi ne na irin ci gaban da za a kai ga cimmawa zuwa karshen shekara. Haka kuma, ba kasar Sin kadai za ta amfana ba, domin wannan sakamako da aka samu a lokaci kalilan, ba karfafa gwiwar duniya kadai zai yi ba, har ma da samar da makoma mai haske ga tattalin arzikin duniya kamar yadda ya saba.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Xi Ya Taya Kim Jong Un Murnar Cikar Jam’iyyar WPK Shekaru 80 Da Kafuwa
Daga Birnin Sin

Xi Ya Taya Kim Jong Un Murnar Cikar Jam’iyyar WPK Shekaru 80 Da Kafuwa

October 10, 2025
An Jinjinawa Tallafin Kamfanonin Sin Ga Tsarin Bunkasa Masana’antun Senegal
Daga Birnin Sin

An Jinjinawa Tallafin Kamfanonin Sin Ga Tsarin Bunkasa Masana’antun Senegal

October 9, 2025
Masu Kallon Fina-Finai Na Sin Sun Gamsu Da Fina-Finan Da Aka Gabatar A Lokacin Hutun Bikin Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar Sin Ta 2025
Daga Birnin Sin

Masu Kallon Fina-Finai Na Sin Sun Gamsu Da Fina-Finan Da Aka Gabatar A Lokacin Hutun Bikin Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar Sin Ta 2025

October 9, 2025
Next Post
An Gano Dajin Da Ya Fi Shekara Miliyan Hudu A Duniya

An Gano Dajin Da Ya Fi Shekara Miliyan Hudu A Duniya

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Taya Kim Jong Un Murnar Cikar Jam’iyyar WPK Shekaru 80 Da Kafuwa

Xi Ya Taya Kim Jong Un Murnar Cikar Jam’iyyar WPK Shekaru 80 Da Kafuwa

October 10, 2025
An Zuba Jarin Dala Biliyan 5.2, An Sa Hannu Kan Yarjejeniyoyi 47 A Taron Tattalin Arziƙin Bauchi 

An Zuba Jarin Dala Biliyan 5.2, An Sa Hannu Kan Yarjejeniyoyi 47 A Taron Tattalin Arziƙin Bauchi 

October 10, 2025
Nijeriya

Haramcin Haƙar Ma’adanai: Majalisa Za Ta Kawo Ƙarshen Asarar Dala Biliyan 9 Duk Shekara

October 10, 2025
Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano

Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano

October 10, 2025
Yadda Rashin Isassun Malaman Turanci Da Lissafi Ke Shafar Ingancin Ilimi A Nijeriya (3)

Yadda Za A Magance Yawaitar Malaman Da Ba Su Cancanta Ba A Nijeriya – TRCN

October 10, 2025
Gwamnatin Katsina Ta Rufe Makarantu 32 Masu Zaman Kansu Da Ba Su Da Lasisi

Gwamnatin Katsina Ta Rufe Makarantu 32 Masu Zaman Kansu Da Ba Su Da Lasisi

October 10, 2025
arziki

Burin ‘Yan Nijeriya Bai Cika Ba Tun Bayan Samun ‘Yancin Kai

October 10, 2025
Matatar dangote

ACF Ta Yi Zargin Shiri Na Musamman Don Rusa Matatar Man Dangote

October 10, 2025
Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus

Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus

October 10, 2025
Gwamnatin Kogi Ta Yaba Wa Tinubu Kan Naɗin Amupitan Shugaban INEC

Gwamnatin Kogi Ta Yaba Wa Tinubu Kan Naɗin Amupitan Shugaban INEC

October 10, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.