Hukumar Kididdiga ta kasar Sin ta samar da alkaluman tattalin arziki na watan Agusta a kwanan nan, alkaluman da suka nuna cewa, tattalin arzikin Sin yana ci gaba da bunkasa ba tare da tangarda ba, musamman a fannin sana’o’in ba da hidima, inda ma’aunin ISP game da ayyukan ba da hidima ya karu da kashi 5.6% idan aka kwatanta da makamancin lokacin shekarar da ta gabata.
Abin lura shi ne, a matsayin wani muhimmin bangare na sana’o’in ba da hidima na zamani, sana’ar al’adu ita ma tana nuna gagarumin ci gaba. A taron dandalin kasa da kasa kan harkokin al’adu na “Golden Panda” da aka gudanar kwanan nan, ministar fasaha, al’adu, yawon bude ido da tattalin arzikin kirkire-kirkire ta Najeriya, Hannatu Musawa, ta yaba wa saurin ci gaban sana’o’in kirkire-kirkire ta Sin, inda ta bayyana cewa, Sin tana hada hangen nesa da kirkira, wanda ya sa ta zama hasken gwarazan al’adu a duniya. Ta kuma bayyana fatan kara karfafa hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Sin a fannoni na kirkire-kirkire da al’adu.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya taba bayyana cewa, “Tattalin arziki shi ne tushen al’adu, inda karfin tattalin arziki ke aza tubali mai inganci ga ayyukan raya al’adu.” Ci gaban tattalin arzikin Sin ba tare da tangarda ba ya kafa tushe mai karfi ga bunkasar al’adu, bunkasar al’adu ta kuma samar da gadar fahimtar juna a tsakanin Sin da sauran kasashe. (Mai zane da rubutu: MINA)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp