Kwanan baya, kafofin watsa labarai na kasar Indiya sun fidda rahotanni cewa, hukumar leken asiri ta kasar Amurka wato CIA na shirin kafa wata kasa a kasar Bangladesh, da kasar Myanmar, da kuma arewa maso gabashin kasar Indiya.
Manazarta na ganin cewa, ana fuskantar matsaloli da dama dake shafar kabilu da addinai da tarihi a arewa maso gabashin kasar Indiya, lamarin da ya sa ake fama da rikice-rikice da tashe-tashen hankula a yankin. Idan da gaske ne hukumar CIA ta kafa wata kasa a yankin, to tabbas zai haddasa karin barazana ga yankin, da kuma haifar da kalubaloli ga kasar Indiya baki daya.
Wasu masanan kasar Indiya sun ce, ko da yake, kasar Amurka da kasar Indiya sun cimma matsayi daya kan wasu batutuwa, a cikin ’yan shekarun baya, kasar Indiya ba ta bi umurnin kasar Amurka kan wasu harkokin kasa da kasa, lamarin da bai yi wa Amurka dadi ba. Shi ya sa, kasar Amurka za ta mayar da martani ga kasar Indiya, kamar yadda CIA ta taba yi cikin kasashen Italiya da Iran da kuma kasar Masar da dai sauransu. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)