• English
  • Business News
Friday, October 24, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Cibiyar Binciken Harkar Noma (IAR) Ta Samar Da Irin Masara Mai Inganci

by Idris Umar
2 years ago
Noma

LABARAI MASU NASABA

Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya

Gwamnatin Jihar Taraba Ta Ayyana Yi Wa Kasuwannin Sayar Da Dabbobi 9 Garanbawul

Cibiyar binciken harkar noma ta Jami’ar Ahamadu Bello da ke Zariya (IAR), ta yi taron gani da ido na fitar da Irin Masara mafi inganci ga manoman wannan kasa baki-daya.

Daya daga cikin wadanda suka jagoraci wannan bincike, Farfesa Rabi’u ya bayyana cibiyar binciken harhar nomar wato, ‘Institute of Agriculture Research’ a matsayin wadda ta fitar da ranar 12 ga watan Satumbar shekarar 2023, domin shaida wa duniya shirinta na ‘TELA MAIZE’, ma’ana rana ta musamman don nuna wa kasarmu da manoman duniya Irin Masara mai suna ‘TELA’, wacce take dauke da sinadarai masu yawan gaske.

  • Duk Da Tazarar Dake Tsakaninmu, Za Mu Iya Jin Dadin Kyakkyawar Wata Tare 
  • Duk Da Tazarar Dake Tsakaninmu, Za Mu Iya Jin Dadin Kyakkyawar Wata Tare 

Ya ce, dalilin gudanar da wannan taro a wannan gona shi ne, domin manoma su shaida banbancin da ke tsakanin sabon Irin ‘TELA MAIZE’, da kuma saura Irin da ake da su a halin yanzu.

Farfesan ya kara da cewa, a wannan gona ana shuka masara kala daban-daban, don tantance abin da cibiyar ke son jama’a su shaida tsakanin sauran Irin masarar da sabo na ‘TELA  MAIZE’.

A kalla manoma daga cibiyoyi da kungiyoyi daban-daban sun gamsu da wannan sabon Iri da wannan cibiya ta kirkiro a zamanace tare da yin jinjina ga wannan nazari na bincike da aka gudanar.

Shi ma a nasa tsokacin, Shugaban Cibiyar Farfesa M.F Ishiyaku, ya ce, “Da farko ina godiya a madadin ‘Institute for Agricultural Research’ ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Samaru Zariya, wadda  ke jin dadin kula da daukar nauyi daga Ma’aikatan Aikin Gona ta tarayya, ina yi muku barka da zuwa wannan hamshakin taro na gani da ido. Ina kuma mika godiyata ta musamman, ga manoma, musamman wadanda suka tari aradu da ka suke karbar fasahohinmu na gwaji, domin tarar aradu da ka ne ka karbi abin da ba ka san ingancinsa ba, saboda ka ba da gaskiya ka jarraba shi, domin ta hanyar ka wani dan’uwanka ma zai gani ya assasa wannan abin, shi ya sa har kullum bincikenmu ba ya cika har sai mun shigo da manoma ciki sun sa mana hannu kafin ya samu karbuwa.”

Saboda haka, ya kamata manoma mu fahimta cewa wannan daya  daga cikin yunkurin da Gwamnatin Tarayya ke yi na rage matsalolin noma a wannan kasa. Daya daga cikin matsalar da manomi ke fuskanta ita ce, matsalar hauhawar farashi ta yadda zai zuba jari a harkarsa ta noma har ya ci riba.

Sa’annan, shugaban kungiyar binciken ya yi bayani dangane da yadda wata tsutsa da ake kira da cema ‘Fall Army Worm’, wadda manoman masara a ‘yan shekarun nan muka wayi gari Allah ya jefo mana ita, wanda idan ba a yi sa’a ba sai ka

wayi gari ka ga gonarka da take da yabanya mai kyau, ana sa rai za a samu abin kirki sai ka ga duk daga zuciyarta ta lalace an yi asarar ta baki-daya.

Har ila yau, babban makasudin wannan taro shi ne, tabbatar wa manoma cewa, tana iya yiwuwa a bullo da ingantaccen Iri na masara, wanda zai jure kansa ba tare da an yi masa feshin

magani ba, ma’ana zai iya jure kansa da kansa. Mun gamsu wannan sabon Iri yana da wannan inganci kwarai da gaske, amma mun zo ne domin mu sake jaddada wannan.

Saboda haka, na ke kara jinjina wa manoman da suka yi fice wajen rungumar sababbin fasahohi ba wannan kawai ba, har ma sauran fasahohi na shekarun baya da muka yi ta yi. Idan za ku iya tunawa, wannan cibiya tamu a wannan shekare ne ta cika shekaru dari da daya cif. A wannan zamani na wannan cibiya tamu, mu muka dauki alhakin yada dukkannin wani ingantaccen aikin noma, kama daga rainon ‘ya’yan itatuwa, hatsi, dawa, gero, masara, wake, waken suya da sauran makamantansu har ya zuwa yanzu din nan, kafin a da aka yi garambawul ga irin nauye-nauyen da aka dora mana a sanadiyar sake kirkiro da wasu cibiyoyin binciken aka dan rage mana nauyi.

Akwai wadanda babu abin da ya hada su da noma, amma ganin irin fa’idar da ake samu a cikinsa ya sa suka yi cincirindo suka

rungume shi, saboda haka ina ga mu wadanda muka gaje shi a matsayin sana’a. Babu shakka, noma yana ba wa ‘yan Nijeriya kusan kashi 66 cikin 100, wanda ya yi daidai da kimanin kusan mutum miliyan 160 aikin yi. Saboda haka, duk wani manomi

da ya samu karuwar tattalin arziki, daidai ya ke da kamar ka dauki wani ma’aikaci aiki ka rika biyan sa albashi duk shekara.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya
Noma Da Kiwo

Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya

October 18, 2025
‘Yansanda Sun Cafke Ɓarayi 13 Tare Da Ƙwato Shanu 27 A Kaduna
Noma Da Kiwo

Gwamnatin Jihar Taraba Ta Ayyana Yi Wa Kasuwannin Sayar Da Dabbobi 9 Garanbawul

October 18, 2025
Dalilin Bankin AfDB Na Yin Hadaka Da WFP Da IFPRI
Noma Da Kiwo

Dalilin Bankin AfDB Na Yin Hadaka Da WFP Da IFPRI

October 18, 2025
Next Post
Bikin Kafuwar Daular Saudiyya Shekara 93: Abubuwan Da Ya Kamata A Sani

Bikin Kafuwar Daular Saudiyya Shekara 93: Abubuwan Da Ya Kamata A Sani

LABARAI MASU NASABA

Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

October 24, 2025
Nnamdi Kanu Ya Sake Bayyana A Kotu Ba Tare Da Lauya Ba, Zai Kare Kansa Da Kansa

Nnamdi Kanu Ya Sake Bayyana A Kotu Ba Tare Da Lauya Ba, Zai Kare Kansa Da Kansa

October 24, 2025
Uba Sani Ya Amince Da Biyan Naira Biliyan ₦2.3 Ga Tsofaffin Ma’aikata Da Iyalansu

Ƙungiyoyin Ma’aikatan Jihar Kaduna Sun Yabawa Gwamna Sani Kan Amincewa Da Sabon Albashin  Ma’aikata

October 24, 2025
Ƙarfin Niyyar Manzon Allah (SAW) Da Matakinsa Na Aƙlul A’ala

Ƙarfin Niyyar Manzon Allah (SAW) Da Matakinsa Na Aƙlul A’ala

October 24, 2025
Gobara Ta Tafka Ɓarna A Kasuwar Shuwaki, Ta Ƙona Fiye da Rumfuna 500 A Kano

Gobara Ta Tafka Ɓarna A Kasuwar Shuwaki, Ta Ƙona Fiye da Rumfuna 500 A Kano

October 24, 2025
Gwarzuwar Shekarar 2025 Sanata Oluremi Tinubu

Gwarzuwar Shekarar 2025 Sanata Oluremi Tinubu

October 24, 2025
Dauda Lawal Gwarzon Gwamnan 2025: Ceto Zamfara Domin Ci Gaba

Dauda Lawal Gwarzon Gwamnan 2025: Ceto Zamfara Domin Ci Gaba

October 24, 2025
Buƙatar Daƙile Badaƙalar Amfani Da Takardun Karatun Bogi A Nijeriya

Buƙatar Daƙile Badaƙalar Amfani Da Takardun Karatun Bogi A Nijeriya

October 24, 2025
Fahimtar Sabon Tunani: Samar Da Wadata Ga Dukkan Jama’a Ta Daidaita Gibin Dake Tsakanin Hamshakai Da Matalauta

Fahimtar Sabon Tunani: Samar Da Wadata Ga Dukkan Jama’a Ta Daidaita Gibin Dake Tsakanin Hamshakai Da Matalauta

October 23, 2025
Shugaban Senegal: Kasar Sin Ta Zama Abin Koyi Ga Kasashe Masu Tasowa

Shugaban Senegal: Kasar Sin Ta Zama Abin Koyi Ga Kasashe Masu Tasowa

October 23, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.