Cibiyar da ke gudanar da bincike a kan tsirrai ta kasa da ke Jihar Gombe (NIHORT), ta bayyana cewa; ta kammala shirin fara gudanar da bincike a kan cututtukan da suka shafi Kankana, wanda hakan ya tilasata wa wasu daga cikin manoman Kankanan a kauyen Bara da ke a Karamar Hukumar Kirfi ta Jihar Bauchi, hijira zuwa Kasar Kamaru.
Mataimaki a sashen cibiyar na Jihar Gombe, Nasiru Usman ne ya bayyana haka, inda ya sanar da cewa; tawagar cibiyar da za ta gudanar da binciken a kan wadannan matsaloli, za su kai ziyara kauyen na Bara; domin tantance bayanai a kan wadannan matsaloli da zummar dakile barazanar kalubalen da noman Kankana a kauyen ke fuskanta.
- Kotu Ta Tsare Mutane 29 Masu Rajin Kafa Kasar Yarbawa A Oyo
- Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Dakatar Da Neman Zama Madaukakiya Tare Da Sake Waiwayar Dokokin Kasa Da Kasa
A cewar Usman, “Za mu kai ziyara kauyen na Bara mu kuma tattauna da manoman Kankanan da suka fuskanci wannan annoba tare da gaza magance ta da kuma duba gonakins nau.”
Ya kara da cewa, “Akwai bukatar mu tantance bayanai tare da gudanar da cikakken bincike a kan wannan kalubale, domin tabbatar da abin da ya jawo wannan matsala, don lalubo mafita”, in ji shi.
Idan za a iya tunawa, a watannin baya ne jaridar Daily Truts ta ruwaito yadda cututtuka da kwari suka tilasta wa wasu manoman Kankana a kauyen na Bara, yin hijira zuwa Kasar Kamaru.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp