Cibiyar harba kumbuna ta Xichang ta kasar Sin dake lardin Sichuan na kudu maso yammacin kasar, ta cimma gagarumar nasara a jiya Asabar, inda ta yi harbi zuwa sararin samaniya a karo na 200.
Rokar Long March-2C ne ta harba rukunin taurarin dan Adam 11 na Geely-02, da misalin karfe 7:37 na safiyar jiya agogon Beijing, inda tuni ta shiga falakinta kamar yadda aka tsara.
- Xi Ya Mika Gaisuwar Bikin Bazara Ga Dukkan Sinawa
- Yawan Jarin Da Kasar Sin Ta Zuba A Ketare A Bara Ya Karu Kamar Yadda Ya Kamata
Cibiyar ta yi harbi na farko ne a shekarar 1984, wanda ke nufin ta dauki shekaru 40 kafin ta kai ga yin na 200, kuma yanzu haka ita ce cibiyar harba kumbuna mafi sauri da ta cimma wannan nasara.
Kuma tun daga wancan lokaci take ta bayar da gudunmuwa ga masana’antar harba kumbuna ta kasar Sin, inda ta samu nasarar harba kumbuna da taurari da rokoki da sauaran kayayyaki zuwa sararin samaniya, kamar kumbun binciken duniyar wata na Chang’e-1 da tauraron dan adam na BeiDou na farko.
Kasar Sin na da cibiyoyin harba kumbuna 3 a doron kasa wadanda suka hada da cibiyar harba taurari ta Jiuquan dake arewa maso yammacin kasar da cibiyar Taiyuan dake arewaci sai ta Xichang dake Sichuan na kudu maso yammacin kasar.
Baya ga haka, akwai kuma daya dake gabar ruwa, wato cibiyar harba kumbuna ta Wenchang dake lardin Hainan na kudancin kasar. Kuma ta kasance karkashin ikon cibiyar harba kumbuna ta Xichang. (Fa’iza Mustapha)