Za a bude taron baje kolin kayayyakin amfanin yau da kullum na kasa da kasa na kasar Sin ko CICPE karo na 5, daga ranar 13 zuwa 18 ga watan Afrilu, a Haikou, babban birnin lardin Hainan dake kudancin kasar Sin.
Mashirya baje kolin wanda ke zaman muhimmin dandali na cinikayya da sayayya a duniya ne suka sanar da hakan yayin wani taron manema labarai a jiya Laraba.
- A Karon Farko, Malaman Jami’ar Sakkwato Sun Tsunduma Yajin Aiki
- Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Bincike Kan Zaftare Albashin Ma’aikata
Baje kolin wanda ma’aikatar kula da cinikayya da gwamnatin lardin Hainan suka shirya, zai kara fadada shigar kasashen waje don a dama da su, tare da gabatar da kayayyakin da aka kirkiro a karon farko.
Taron wanda zai mayar da hankali kan bangarorin da suka shafi kirkirarriyar basira ta AI da zirga-zirgar jirage da na’urori a kusa da doron kasa da motoci na zamani da fasahar sadarwa a bangaren kiwon lafiya, ya dace sosai da manufofin kirkire-kirkire da Sin ke ba fifiko. Kana manyan kamfanonin fasaha kamar Huawei da iFLYTEK da Tesla, za su gabatar da wasu fasahohi na zamani a wadannan bangarori.
Baje kolin zai gudana ne a babbar cibiyar nune-nune da taruka ta kasa da kasa dake Hainan. Kuma za a kara yankunan sayayya ba tare da biyan haraji ba a rukunin shagunan sayar da kayayyakin kasashen waje ba tare da haraji ba, wadanda ke Haikou da Sanya. Haka kuma, za a gabatar da nune-nune jiragen ruwa a Sanya.
Bugu da kari, masu baje koli na cikin gida za su gabatar da kayayyaki na alfarma da wadanda aka samar a cikin gida, kuma wani bangare na baje kolin zai mayar da hankali ga hada masu sayayya na kasashen ketare da masu samar da kayayyaki na kasar Sin ta hanyoyin da aka tsara na zuba jari. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp