Shugaban Majalisar Amintattu Na Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF), Alhaji Bashir M. Dalhatu, Wazirin Dutse, ya jaddada aniyar kungiyar na samar da hadin kai da bin ka’idojin gudanarwa tsakanin mambobin kungiyar yayin da ake shirin bikin cikar shekaru 25 da kafuwarta watan Nuwamba 2025.
Ya bayyana haka ne yayin jawabin da ya gabatar a taron majalisar amintattu da aka gudanar a babban ofishin ACF da ke Kaduna.
- Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci
- Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk
Alhaji Dalhatu ya jaddada bukatar daidaito da taka-tsantsan wajen isar da sako ga jama’a musamman ga jami’an kungiyar da ke hulɗa da kafafen watsa labarai gabanin babban zaben 2027.
Ya gargadi masu kafa kungiyoyi daban-daban a Arewa, yana kiran irin waɗannan ƙungiyoyi “barazana ga haɗin kan Arewa.” Haka kuma ya yaba wa sojojin Nijeriya bisa kokarinsu da sadaukarwa wajen yaki da matsalar tsaro.
Alhaji Dalhatu ya kuma yi Allah wadai da “ƙungiyoyin marasa kishin ƙasa” da suka jawo rikicin baya-bayan nan a matatar mai ta Dangote, tare da kira ga Gwamnatin Tarayya da ta shiga tsakani.
A cewarsa, kwanan nan an samu rikice-rikicen maganganu masu karo da juna daga wasu jami’an ACF a matakin kasa da jihohi, wanda hakan ya sa dole a kafa tsarin sadarwa mai tsauri. “Majalisar Amintattu tana da ikon da nauyin
Ya bayyana cewa taron, wanda shugabannin jihohi, sakatarori, da mambobin Arewa 100% Focus Group suka halarta, zai tattauna kan manyan batutuwa da suka shafi tsarin sadarwa na jami’an ACF da kuma shirye-shiryen bikin zagayowar cikar shekaru 25.