Kwanakin baya ne kamfanin ‘Retail Supermarkets Nigeria Limited’ mamallakin katafaren shagon sayar da kayan masarurin nan mai suna ‘Shoprite Mall’ ya sanar da aniyarsa na dakatar da harkokinsa a Kano daga ranar 14 ga watan Janairu na sabuwar shekara 2024. Bayanin haka yana kunshe ne a takardar sanarwa da masu gudanar da kamfanin suka raba wa manena labarai.
Katafaren shagon da ke harkokinsa a ‘Ado Bayero Mall’ ya ce, zai dakatar da harkokinsa ne saboda karayar tattalin arziki da shagon ke fuskanta da kuma yadda harkokin kasuwanci ke kara fuskantar tarnaki a sassan kasar nan.
- Bankwana Da 2023: Yamutsin Siyasa Da Zabubbuka
- Samar Da Tsaro: Ribadu Ya Yaba Wa Sarakunan Gargajiya A Adamawa
Takardar sanarwa ta kuma ce, shawarar ficewa daga Nijeriya abin takaici ne kwararai da gaske amma kuma yana da matukar muhimmanci gare su, ‘Za mu dakatar da dukkan ma’aikatan da ke aiki a shagon da zaran mun daina aiki a jihar”.
Amma kuma bayan wadanna dalila da masu gudanar da shagon suka bayyana an kuma fahimci cewa, akwai wasu dalilai na karkashin kasa da suka sanya dole Shoprite ya dakatar tare da ficewa daga Nijeriya.
Bayanin ya nuna cewa, cikin manya-manyan dalilan sun hada da kudin haya na Naira miliyan 66 da suke biya a duk wata bayan kuma kudin wutar lantarki da na gudanar da shagon da na yau da kullum da kuma kudin albashin ma’aikata.
Kamfanin na biya naira miliyan 792 in aka hada da albashin ma’aikata da na wutar lantarki da sauransu.