Yayin da ‘yan jarida da dama a faɗin ƙasar nan ke ci gaba da gudanar da bukukuwan murnar cika shekaru 70 da kafuwar ƙungiyar ‘yan jarida ta Nijeriya (NUJ), Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya miƙa saƙon taya murna a garesu, inda ya yaba da rawar da suke takawa wajen ci gaban jihar da ƙasa baki ɗaya.
A sakonsa na fatan alheri da kakakinsa Isma’ila Uba Misilli ya fitar a ranar Laraba, Gwamna Inuwa Yahaya ya yabawa ‘yan jarida a matsayin manyan abokan hulɗa a tafiyar haɗin gwiwa don samun kyakkyawar makoma ga Nijeriya.
- An Gudanar Da Tarukan Tattaunawa Na Kasa Da Kasa Masu Jigon “Sin A Yanayin Bazara” A Turkiya Da Colombia
- Wakilin Sin Ya Yi Allah Wadai Kan Sabon Yaki Da Isra’ila Ta Tayar A Zirin Gaza
Gwamnan ya kuma yabawa shugaban ƙungiyar ‘yan jaridan ta ƙasa NUJ, Kwamared Alhassan Yahya Abdullahi, bisa namijin ƙoƙarin da yake yi na ƙarfafa ƙungiyar da kuma gina nasarorin da ƙungiyar ta cimma tun daga kafuwarta zuwa yanzu.
Ya kuma nuna jin daɗinsa da irin nasarorin da aka samu a ƙarƙashin jagorancin Kwamared Alhassan Yahayan, inda ya ce an ɗora ƙungiyar kan kyakkyawan turbar da ya kamata don ta ci gaba da taka rawar gani wajen bunƙasa aikin jarida a Nijeriya.
Yahaya ya jaddada cewa akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin gwamnatin Jihar Gombe da ‘yan jarida, yana mai bada tabbacin cewa wannan kyakkyawar alaƙa da haɗin gwiwa za su kasance ginshiƙin gudanar da mulki a jihar.
“Mu a Jihar Gombe muna alfahari da daɗaɗɗiyar dangantakar da muka ƙulla da ‘yan jarida; ‘yan jarida abokan aikinmu ne masu ƙima a fagen kawo ci gaba, kuma muna ci gaba da jajircewa wajen ganin sun ci gaba da yin aiki a yanayin da zai bunƙasa sana’o’insu da ‘yancinsu,” inji Gwamna Inuwa Yahaya.
Ya kuma bada tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da haɗa gwiwa da NUJ da sauran ƙungiyoyin yaɗa labarai don ba su damar ci gaba da kuma gudanar da muhimmiyar rawar da suke takawa wajen ankarar da gwamnati da wayar da kan jama’a.
Gwamna Inuwa ya ƙara da cewa, “Gudunmawar da kuka bayar na da matuƙar muhimmanci wajen inganta demokraɗiyya, da riƙon amana, da kuma shugabanci na gari a Nijeriya, muna godiya da irin rawar da kuke takawa wajen faɗakar da jama’a, da kare gaskiya, da kuma inganta manufofin gaskiya da adalci,” in ji Gwamna Inuwa Yahaya.
Ya kuma jaddada ƙudurin gwamnatin jihar na yin haɗin gwiwa mai ɗorewa da ‘yan jarida, inda ya jaddada muhimmancinsu wajen ci gaban Jihar Gombe dama Nijeriya baki ɗaya.
“Muna fatan ƙara ƙarfafa haɗin gwiwarmu da NUJ, kuma muna da yaƙinin cewa, tare, za mu ci gaba da gina ƙasa mai wadata, zaman lafiya da ci gaba,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp