Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya nuna matukar damuwarsa kan yadda ambaliyar ruwa ta mamaye wasu sassan Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Ambaliyar ruwan mafi muni a cikin shekaru da dama ta raba dubban mazauna yankin tare da mamaye muhimman wurare irin su ofishin hukumar kar ta kwana, da gidan tarihi da kuma asibitin koyarwa na Maiduguri.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, Bayo Onanuga, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, ya ce, shugaba Tinubu ya umarci hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) da ta gaggauta tura kayan aikinta domin taimakawa wadanda abin ya shafa.
Shugaban ya kuma yi kira da a gaggauta kwashe wadanda bala’in ya Ɗaiɗaita.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp