Mambobin kungiyar Malaman jami’oi, wadanda suka cikn yajin aikin gargadi na kwana 14 ko mako biyu wanda aka fara ranar Litinin, sun nuna rashin jin dadinsu yadda farsesohi fiye da 309 suka bar Jami’oin gwamnati a watanni tara da suka wuce.
Shugaban kungiyar na shiyyar Sakkwato, Kebbi, Zamfara Katsina, Farfesa. Abubakar Sabo, shi ne ya bayyana irin yadda Farfesoshin suke barin jami’oin a taron da suka yi kan yadda lamarin yake, wanda Jami’ar Usman Danfodiyo ta shirya a osfishin kungiyar na jami’ar.
- JIBWIS FCT Ta Yi Taron Yaye Iyaye Mata Da Suka Kammala Koyon Sana’o’i
- Iwobi Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Firimiya
Sabo yace yadda manyan Malaman Jami’oin suke barin bangaren koyarwa suna zuwa neman wuraren da suka fi galaba a kasashen waje lamarin abin takaici ne “yadda ake asarar manyan kwararrun” irin hakan kuma wata babbar barazana ce ga Jami’oin gwamnati.Ya ce yawancin kwararrun Malaman sun koma kasashen London, Saudi Arebiya, Kamaru da kuma wasu kasashe.
Ya ce “Daga wancan lokacin zuwa yanzu, mun rasa Farsesoshi 309,wasu sun je Jami’oi masu zaman kansu a Nijeriya, sauran wasu sun je London, Saudi Arebiya, Kameroon da kuma wasu kasashe.Kwarrunmu wadanda babban jari ne suna barin aiki saboda sharuddan aikinsu babu wani abin jin dadin da zai sasu ci gaba da kasancewa wuraren aikinsu na koyarwa kamar yadda ya ce,”.
Sabo ya bayyana cewa kungiyar za ta fara yajin aikin mako biyu daga ranar Litinin, idan har gwamnatin tarayya ta ci gaba watsi da maganar bukatunta da kuma inganta masu sharuddan aiki.
“Mun yi shiru har abin ya wuce misali.Hakkin mune nu ceto jami’oin gwamnati. Idan har gwamnati ta ci gaba da yin biris da mu, ba zamu ci gaba da sa ido ba yayin da lamarin ilimi yana kara durkushewa.
“Da muka bada wa’adin mako biyu, gwamnati ta farakiran waya ne, daganan suka fara kiran kungiyoyi kamar na makarantun fasaha, da Kwalejojin ilimi domin su kara dagula lamarin cewar akwai wani kokarin da ake na kawo matsala samar da matsaloli kan kasafin kudin ilimi domin dakushe irin gwagwarmayar samun bukatunsu da suke kamar yadda ya yi zargi,”.
Tun farko ne Shugaban kungiyar na ASUU-UDUS, Farfesa. Muhammad Almustapha, ya ce taron an kira shi ne domin a sanar da ‘yan Nijeriya dangane da irin koma bayan da ake samu a ilmin Jami’oi, da kuma gazawar gwamnati ta cika ma kungiyar alkawuran data yi.
“Shekarun da suka gabata, kungiyar ASUU ta saba da tafiye- tafiye yajin aiki, saboda yana da matukar wuya gwamnati ta cika alkawuran da ta yi. Abin ya zama alkawari bias wani alkawarin da, ba za’a cika ba duk kuma wani tunanin da kungiyar take abin ya zama kanzon Kurege kama yadda ya jaddada”.
Kungiyar ta yi kira da gwamnati ta dauki mataki na gaggawa domin ta kawo karshe karshen yadda kwararru suke barin aikin koyarwa, domin a shawo kan kara lalacewar ilimin jami’a a Nijeriya.