Kimanin Mutum miliyan hudu ne suka ziyarci Kabarin Manzon Allah SAW a Madina cikin wata ukun farko na shekarar Musulunci ta bana.
Shafin da ke kula da Masallatai Biyu Masu Daraja na Saudiyya na Makkah da Madina, Haramain Sharifain ne ya bayyana hakan a Facebook ranar Lahadi.
Kazalika shafin ya ce yawan wadanda suka ziyarci Raudah kuwa da ke cikin Masallacin Manzon Allah ya haura miliyan huɗu a ɗan tsakanin.
Daga BBC Hausa