Shugabannin kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC da TUC sun sanar da tsunduma yajin aikin gama gari a fadin kasar nan a ranar Talata mai zuwa 14 ga watan Nuwamba 2023.
Shugabannin kungiyoyin biyu, sun cimma wannan matsaya ne bayan wani taron majalisar zartarwar kungiyar ta kasa na musamman da aka yi ranar Talata a Abuja.
- Kama Shugaban NLC Ya Haifar Da Cece-Kuce A Nijeriya
- Ka Nemi Sana’a Siyasa Ba Taka Ba Ce,Tinubu Ga Peter Obi
Matakin da kungiyar kwadagon ta dauka ya biyo bayan cin zarafin da aka yi wa shugaban NLC na kasa, Joe Ajaero a makon da ya gabata a jihar Imo.
Kungiyar kwadagon ta zargi kwamishinan ‘yansandan jihar Imo, Mohammed Barde da hannu wajen cin zarafin Ajaero kwanan nan a Owerri, babban birnin jihar Imo.
Kungiyar Kwadago a ranar Juma’ar da ta gabata ta baiwa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki biyar domin ta maye gurbin kwamishinan ‘yansandan, yayin da ta kuma zargi Gwamna Hope Uzodimma da ke neman a sake zabensa da harin da aka kai wa Ajaero duk da cewa, Gwamnan ya ce ba shi da hannu kan cin zarafin shugaban kungiyar kwadagon.
Kungiyar Kwadagon ta kuma bukaci a kama tare da gurfanar da wasu daga cikin hadiman gwamnan inda ta yi barazanar daukar wani mataki na tsunduma yajin aiki a duk fadin Nijeriya idan ba a aiwatar da bukatunsu ba.