An fitar da alkaluman cinikayya tsakanin Sin da kasashen waje a watanni 7 na farkon shekarar bana a jiya Laraba, inda alkaluman suka nuna cewa, jimilar darajar kayayyakin shige da fice da Sin ta yi cinikayyarsu, ta kai yuan triliyan 24.83, karuwar kaso 6.2 cikin dari bisa makamancin lokacin a bara. Tare da saurin karuwar shige da fice da ya bunkasa baki daya a rabin farkon shekarar bana, kana ma’aunin cinikayya tsakanin Sin da kasashen waje a watanni 7 na farkon bana ya sake shiga sabon matsayi mafi girma a tarihi bisa makamancin lokaci na bara.
Cinikayya tsakanin Sin da waje ta ci gaba da karuwa, kuma hakan ba kawai ya nuna jurewa, da kuzarin tattalin arzikin Sin ba ne, har ma ya haifar da alherai da yawa ga duniya. Abu mai kyau da Sin ta kawo wa duniya da farko shi ne damammakin babbar kasuwa ta Sin, wanda ke kawo sauki ga kasa da kasa wajen raba kasuwar Sin tare. A sa’i daya kuma, Sin ta inganta sabon karfin samar da hajoji, da hidimomi masu karko bisa halin da ake ciki, wanda ya samar da sabon karfi ga ci gaban kasa da kasa. Idan an yi hangen nesa, cinikayya tsakanin Sin da kasashen waje ta ba da gudummawa ga kiyaye kwanciyar hankali a tsarin sarrafa hajojin masana’antu, da ma tsarin samar da hajoji na kasa da kasa. (Safiyah Ma)