Wani rahoton hadin gwiwa na kamfanonin Bain & Company, da Kantar Worldpanel, masu bibiyar harkokin da suka shafi cinikayya, ya nuna cewa, cinikayyar kananan kayayyakin amfanin al’umma na yau da kullum na gudana cikin yanayin karko a kasar Sin, duk da kalubalen da ake fuskanta na bazuwar annobar COVID-19.
Rahoton ya ce sashen cinikayyar kananan kayayyakin amfanin al’umma na yau da kullum na kasar Sin ko FMCG a takaice, ya jurewa matsaloli masu alaka da samar da kayayyaki, da koma bayan tattalin arziki, saboda matsin da annobar COVID-19 ta haifar.
Kaza lika rahoton ya ce sashen na FMCG, ya bunkasa da kaso 3.6 bisa dari a shekara guda, tsakanin rubu’o’i 3 na farkon shekarar 2022. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan daga CMG Hausa)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp