Jimilar kayayyakin da Sin ta yi shige da ficensu ya karu da kaso 4.7 cikin dari zuwa yuan triliyan 16.77 a watanni 5 na farkon bana, wanda ya nuna cewa bangaren na ci gaba da nuna juriya duk da raguwar bukatu a waje.
Hukumar kwastam ta kasar Sin ta bayyana cewa, yawan kayayyakin da ake fitarwa ya karu da kaso 8.1 cikin dari a kan na bara, yayin da na kayayyakin da ake shigo da su ya karu da 0.5 cikin dari, a cikin watanni 5 na farkon bana.
Ma’aikatar kula da cinikayya ta kasar ta bayyana a ranar Litinin cewa, kasar na gina wata budaddiyar kasuwar bai daya, irin ta kasa da kasa a cikin gida.
A cewar ma’aikatar, kasuwar ta bai daya, za ta samarwa bangarorin kasuwanci daban-daban, ciki har da kamfanoni masu jarin waje, ingantaccen muhallin kauswanci mai karin girma. (Fa’iza Mustapha)