A gabar da kayayyakin da ake fitarwa zuwa kasashen ketare suka kai wani sabon matsayi, a hannu guda kuma jimillar cinikayyar ketare baki daya ta daidaita, kasuwar cinikayyar waje ta kasar Sin ta samu karbuwa matuka, duk da hauhawar farashin kayayyaki da raunin ci gaban tattalin arziki da cinikayya da ake fuskanta a duk duniya.
Alkaluman da babbar hukumar kwastam ta kasar Sin (GAC) ta fitar sun nuna Talatar nan cewa, yawan kayayyakin da kasar ke fitarwa zuwa kasashen waje, ya karu da kashi 0.9 bisa 100 a cikin watannin biyun farkon bana kan shekarar da ta gabata, zuwa kudin Sin RMB yuan triliyan 3.5 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 506.1.
Cinikayyar kayyakin waje na kasar Sin, ya ragu da kashi 0.8 bisa 100 a shekara, zuwa kudin Sin RMB yuan triliyan 6.18. Darajar kayayyakin da aka shigo da su daga waje zuwa cikin kasar a daidai wannan lokaci kuwa, sun kai kudin Sin RMB yuan triliyan 2.68, wanda ya ragu da kashi 2.9 cikin 100, idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata.
Alkaluman da aka fitar sun nuna cewa, darajar rarar cinikin kasar ta kai kudin Sin RMB yuan biliyan 810.32, wanda ya karu da kashi 16.2 bisa dari kan makamancin lokaci na bara.
Wani jami’in babbar hukumar kwastan ta kasar ( GAC) Lyu Daliang ya bayyana cewa, cinikin waje na kasar Sin, ya jure kalubale da dama, kamar raunata bukatun ketare, ya ci gaba da taimakawa bunkasuwar tattalin arzikin kasar. (Ibrahim)