Hukumar kwastam ta kasar Sin, ta ce a shekarar 2024 da ta shude, cinikayyar waje da kasar Sin ta gudanar ta kai sabon matsayi, yayin da kasar ta biyu a karfin tattalin arziki ta kara karfafa matsayinta, na kasancewa a sahun gaba a fannin cinikayya tsakanin sassan kasa da kasa.
Wasu alkaluma da hukumar ta fitar a yau Litinin din nan, sun nuna yadda darajar hada-hadar shige da ficen hajoji ta kasar Sin a shekarar ta bara, ta kai kudin kasar yuan tiriliyan 43.85, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 6.1, karuwar da ta kai ta kaso 5 bisa dari a shekara.
Da yaka tsokaci game da hakan, yayin taron manema labarai da ya gudana a yau a birnin Beijing, mataimakin shugaban hukumar ta kwastam Wang Lingjun, ya ce cinikayyar waje ta Sin a shekarar 2024, ta bunkasa cikin sauri idan an kwatanta da sauran manyan rukunoni masu karfin tattalin arziki. Kaza lika, Sin ta zamo babbar abokiyar kasuwancin kasashe da yankunan duniya sama da 150, kuma tana ci gaba da fadada kawance da sassa daban daban a fannin inganta cinikayyar waje. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp