Alkaluman kididdiga da hukumar kwastam ta kasar Sin ta fitar a Litinin din nan, sun nuna yadda cinikayyar jimillar hajojin shige da fice na kasar ta karu da kaso 3.6 bisa dari cikin watanni 11 na farkon shekarar bana, daidai da karuwar kudin kasar har yuan tiriliyan 41.21, wato kusan dalar Amurka tiriliyan 5.82.
Karuwar hakan ta gudana bisa daidaito, idan an kwatanta da ta kaso 3.6 bisa dari da kasar ta samu cikin watanni 10 na farkon shekarar ta 2025.
Kazalika a watan Nuwamba kadai, alkaluman adadin hajojin shige da fice na Sin sun daga da kaso 4.1 bisa dari a mizanin shekara zuwa kudin kasar yuan tiriliyan 3.9. (Saminu Alhassan)
ADVERTISEMENT














