Cinikayya dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ta samu ci gaba yadda ya kamata a cikin watanni 7 na farkon shekarar bana, kamar yadda alkuluma suka nuna a yau Laraba.
Alkaluman babbar hukumar kwastam ta kasar Sin sun nuna cewa, cinikayya tsakanin Sin da Afrika daga watan Janairu zuwa Yuli ta karu da kashi 7.4 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin wannan lokaci na bara zuwa yuan triliyan 1.14 kimanin dalar Amurka biliyan 158.36.
Kasar Sin ta kasance abokiyar cinikayyar Afirka mafi girma cikin shekaru goma da suka gabata, inda a shekarar 2022 cinikayya tsakanin bangarorin biyu ta kai yuan triliyan 1.87, karin kashi 14.8 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.
Alkaluman kwastam sun nuna cewa, a cikin watanni 7 na farkon bana, darajar kayayyakin da kasar ke fitarwa zuwa kasashen Afirka ta karu da kashi 20 cikin dari a shekara zuwa Yuan triliyan 709.59, yayin da darajar kayayyakin da ake shigowa da su kasar daga kasashen Afirka ta kai yuan biliyan 426.65.
Kasar Sin ta kasance kasa mafi girma, inda kasashen Afirka suke fitar da kayayyakin dake hada da danyen mai, da karafa da yashi, da kuma amfanin gona.
A cikin dukkan kasashen Afirka, Afirka ta Kudu ta kasance abokiyar cinikayyar kasar Sin mafi girma a cikin watanni bakwai na farkon bana, sai Najeriya da Angola suke biyo bayanta. (Mai fassara: Yahaya)