Bayanin da Hukumar Haraji ta Kasar Sin ta fitar ya nuna cewa, a rabin farko na wannan shekara, kudaden cinikin da kamfanoni a duk fadin kasar suke samu ya ci gaba da karuwa cikin kwanciyar hankali. Masana’antu sun sami ingantaccen ci gaba yayin da manufofin “sabunta manyan kayan aiki na kasa” da “Maye gurbin kayan amfani da suka tsufa da sababbi” suka yi tasiri sosai.
Kudin da aka samu a bangaren sana’ar kere-kere ya karu da sauri fiye da matsakaicin karuwar dukkan kamfanoni da kashi 1.5%.
Wannan ya tabbatar da cewa masana’antu su ne tushen karfafa tattalin arzikin kasar.
Kazalika, masana’antun kirkire-kirkire sun kara habaka, inda kudaden da aka samu a bangaren sayar da kayayyaki na masana’antun kimiyya mai inganci ya karu da kashi 14.3% idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. Abin da ya nuna ci gaba mai sauri a wadannan bangarori. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp