Hukumar kwastam ta kasar Sin ta fitar da alkaluma a yau Talata, wanda ke nuna cewa, daga watan Jarairu zuwa Nuwamban bana, yawan darajar cinikin shige da fice na kasar Sin ya kai dalar Amurka kimanin tiriliyan 5.5, wanda ya karu da kashi 4.9% bisa na makamancin lokaci na bara, kuma daga cikin adadin cinikin fitar da kayayyaki ketare ya kai kimanin dalar Amurka triliyan 3.2, yayin da cinikin shigo da kayayyaki daga waje ya kai kimanin dalar Amurka triliyan 2.3, adadin da ya karu da kashi 6.7%, da 2.4% bisa na makamancin lokaci na bara. Alkaluman dake bayyana cewa, cinikin shige da fice na gudana yadda ya kamata ba tare da tangarda ba a wadannan lokuta. (Amina Xu)