Daga watan Jarairu zuwa Nuwamban bana, yawan darajar cinikin shige da ficen kasar Sin ya kai kimanin dalar Amurka triliyan 5.5, wanda ya karu da kashi 4.9% bisa na makamancin lokacin bara, daga ciki, cinikin fitar da hajoji zuwa kasashen waje ya karu da kashi 6.7%, yayin da cinikin shigo da kayayyaki cikin gida ya karu da kashi 2.4%. Alkaluma na bayyana bunkasuwar cinikin Sin yadda ya kamata ba tare da tangarda ba.
Idan mun yi hange a duk fadin duniya, samun irin wannan ci gaba ba abu ne mai sauki ba. Wasu tsoffin sana’o’i a kasar Sin, ciki har da dakon sundukai, da jiragen ruwa sun samu sabuwar bunkasuwa, duba da cewa, sabbin sana’o’i ciki har da sabon karfin samar da hajoji, da hidimomi masu karko, da motoci masu aiki da makamashi mai tsabta, da batiran Lithium, da kayayyakin samar da lantarki ta amfani da hasken rana da Sin take kokarin rayawa, na jagorantar bunkasuwar cinikin shige da ficenta. Hakan ya sa kirkire-kirkiren da Sin take yi a wadannan bangarori na samun karbuwa matuka a duniya.
- Tinubu Na Son Ganin Kowa Ya Daina Kwana Da Yunwa A Nijeriya – Minista
- Shehu Sani Ya Ƙalubalanci Sarki Sanusi II Kan Maganar ‘Mari’
Ba ingatattun kayayyaki kadai Sin take samarwa ga duk fadin duniya ba, tana kuma more babbar kasuwarta, da damammaki masu kyau ga dukkanin fadin duniya.
Kaza lika, gwamnatin Sin ta kulla yarejejeniya da mabambantan bangarori, don habaka kasuwannin kasa da kasa, ciki har da kasashe masu alaka da shawarar “ziri daya da hanya daya”. A wani bangare kuma tana kokarin shigo da ingatattun kayayyaki daga waje.
Ci gaban cinikin Sin mai dorewa na bayyana kuzari, da karfin tattalin arzikin kasar, wanda hakan ya baiwa dukkanin fadin duniya damammaki da tabbaci masu kyau.
Shaidu na hakika na nuna cewa, Sin na bude kofarta ga ketare yayin da take kokarin samun bunkasuwa, kana tana dukufa kan kafa tsarin tattalin arziki mai bude kofa. Kuma za ta ci gaba da bude kofarta ga ketare, da cudanya da ka’idojin ciniki na duniya masu inganci, don raya yanayinta na ciniki mai kyau, da samar da karin damammaki ga ketare, ta yadda za su more ci gaban da take samu tare. (Amina Xu)