Jimillar kayayyakin da kasar Sin ta shigo da su da kuma wadanda ta fitar da su da kudin yuan ya karu da kashi 1.3 cikin dari, a rubu’in farkon bana idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara, lamarin da ya nuna samun ci gaba cikin kwanciyar hankali da juriya, duk da guguwar rashin tabbas daga waje.
Babbar hukumar kwastam ta kasar (GAC) ce ta bayyana hakan a yau Litinin, inda ta ce kayayyakin da kasar Sin ta fitar da su a wannan lokaci ya karu da kaso 6.9 cikin dari zuwa yuan triliyan 6.13 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 850.1, yayin da yawan kayayyakin da ta shigo da su ya ragu da kaso 6 cikin dari zuwa yuan tiriliyan 4.17.
Mataimakin shugaban hukumar ta GAC, Wang Lingjun, ya shaidawa taron manema labarai cewa, duk da raunin da ake samu a ci gaban tattalin arzikin duniya, da karfafa kariyar cinikayya, da kuma rikicin siyasa na shiyya, cinikin waje na kasar Sin ya samu ci gaba bisa daidaito kuma mai inganci a bana. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp