A yayin taron manema labarai da aka saba yi yau da kullum da ya gudana a yau Alhamis, kakakin ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin He Yongqian ta bayyana cewa, harkokin cinikayyar waje na kasar Sin na ci gaba da samun bunkasa a bana, inda aka samu karuwar kashi 3.5 cikin dari a cikin watanni 7 na farkon bana, wanda ya nuna an samu ci gaba mai yawa da kuma inganci.
He Yongqian ta bayyana cewa, a cikin watanni bakwai na farkon wannan shekarar, kayayyakin shige da fice da Sin ta yi cinikayyarsu tare da kasuwanni masu tasowa da sauransu, sun karu da kashi 5 cikin dari, inda adadin ya kai kashi 65.5 cikin dari a halin yanzu. A ciki kuma. kayayyakin shige da fice da Sin ta yi cinikayyarsu tare da ASEAN sun karu da kashi 9.4 cikin dari, kayayyakin shige da fice da Sin ta yi cinikayyarsu da kasashen Afirka kuwa sun karu da kashi 17.2 cikin dari.
Ta kuma bayyana cewa, ya zuwa karshen watan Yuli, yawan masu yin kasuwanci ta yanar gizo a yankunan karkara a kasar Sin ya zarce miliyan 19.5. Bugu da kari, adadin sayayyar kayayyaki ta yanar gizo a karkara ya karu da kashi 6.4 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp