Kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa (ASUU) ta ce, yunkurin gwamnatin tarayya na zaftare kaso 40 cikin 100 na kudaden shigan jami’o’i kai tsaye zai kassara tsarin jami’o’in Nijeriya.
A watan Oktoba, ministan kudi ya sanar da cibiyoyin ilimi da suke sassan kasar nan cewa kasar na shirin fara tsaftare kaso 40 cikin dari na kudaden shigansu (IGR).
- ASUU Ta Bai Wa ‘Yan Gudun Hijira 320 Tallafin Kayan Abinci A Katsina
- Saboda Kishin Ilimi Muka Raba Wa Makarantun Kano Littafai Sama Da Miliyan 2 – Kwamishinan Addini
A wata sanarwa dauke da sanya hannun shugabanta ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, bayan zaman majalisar kolin kungiyar da ya gudana a jami’ar Jihar Kaduna, ya yi bayanin cewa jami’o’in ba hukumomin samar da kudaden shiga ba ne.
Ya kara da cewa kudaden makaranta da dalibai ke biya ana amfani da su ne wajen samar da kayan aiki domin tabbatar da horas da daliban da ba su ilimi da tarbiyya yadda ya dace.
A cewar sanarwar, sun zauna ne domin tattauna muhimman batutuwan da suka shafi tsarin jami’o’in kasar nan.
Osodeke ya shawarci gwamnatin tarayya da ta cire jami’o’i daga tsarin da take yunkurin zaftare musu kaso 40 na cikin kudaden shigarsu.
Ya ce ASUU ta yi tir da matakin kokarin tilasta cire kason kudaden shigana jami’o’in, yana mai cewa hakan zai kara dakula tsarin jami’o’in Nijeriya.
“Domin cire kowace irin kokonto, jami’o’i ba cibiyoyin tara kudaden shiga ba ne, saboda kudaden makaranta da dalibai ke biya ana amfani da su ne wajen sayen kayayyakin aikin da ake koyar da su.
“Don haka muna kira ga masu ruwa da tsaki kan cire wannan kason da su gaggauta cire jami’o’i daga wannan tsarin domin tabbatar da kyautata harkokin ilimi a fadin kasar nan,” ya shaida.