Bayan taron majalisar zartarwa na mako-mako, gwamnatin jihar Edo ta ware naira miliyan 500 domin rabawa marasa karfi a jihar wanda kowanne mutum zai samu naira 20,000.
Za a fara aiwatar da shirin ne daga watan Satumba, tallafin za a bayar ne domin rage radadin cire tallafin mai wanda ya haifar da hauhawar farashin kayayyakin masarufi a fadin Nijeriya.
Kwamishinan sadarwa da wayar da kan jama’a na jihar, Mista Chris Osa Nehikhare ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar jim kadan bayan kammala taron majalisar.
Ya ce, za a karbo Naira miliyan 500 din ne daga asusun tattara kudaden shiga na jihar (IGR), ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar na da tabbatacciyar bayanai na marasa karfi a jihar, wanda aka tattaro a shekarar 2019 zuwa 2021 tare da hadin guiwar Bankin Duniya.