Gwamnatin Jigawa ta ware Naira miliyan 50 don tallafa wa mata 1,000 masu kananan sana’o’i, domin rage radadin cire tallafin man fetur a kasuwancinsu.
Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na Jihar, Alhaji Sagir Musa ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a karshen taron Majalisar Zartaswar Jihar, ranar Laraba a Dutse.
Ya ce, amincewar ta biyo bayan wata takardar bukata da kwamishiniyar harkokin mata, Hajiya Hadiza Abdulwahab ta gabatar wa majalisar.
A cewarsa, wannan yunkurin zai rage radadin cire tallafin man fetur a bangaren mata masu kananan sana’o’i.
“Majalisar ta umurci ma’aikatar da ta zabo Mata 1,000 masu kananan sana’o’i don tallafa musu da Naira 50,000 kowacce, domin bunkasa sana’arsu.
“Wannan shirin farko ne, shirye-shirye da ayyuka masu yawa na nan tafe, don tallafa wa jama’a a yunkurin gwamnatin na rage radadin cire tallafin man fetur,” in ji shi.