• English
  • Business News
Saturday, September 20, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Cire Tallafin Mai: Babu Shirin Karin Kudin Kiran Waya – NCC

by Khalid Idris Doya
2 years ago
in Labarai
0
Cire Tallafin Mai: Babu Shirin Karin Kudin Kiran Waya – NCC
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Hukumar kula da harkokin sadarwa ta Nijeriya (NCC) ta nanata cewa babu wani shirin kara kudin kiran wayar tarho sakamakon cire tallafin Mai.

Babban mataimakin shugaban hukumar NCC, Farfesa Umar Garba Danbatta ne ya bada wannan tabbacin a karshen mako yayin da yake amsar lambar yabon Titans of Tech (ToT) a jihar Legas.

  • Rundunar ‘Yan Sanda Sun Cafke Dan Yahoo Da Ya Kware Kan Cutar ‘Yan Kasar Hungary A Nijeriya

Dambatta na cewa: “NCC ta fada cewa ba ta shirya kara kudin kiran waya a yanzu sakamakon cire tallafin Mai ba. Irin wannan matakin ya rage ga dukkanin kamfanonin sadarwa su duba abun da za su yanke. Mun tattauna sosai da dukkanin kamfanonin. Don haka wannan ya rage musu su cimma matsaya. Muna tafiyar da aiki da shigo da kowa cikin lamura a NCC. Ba mu yi magana kan karin kudin wayar tarho ba ya zuwa yanzu.”

Dambatta wanda ya samu wakilcin shugaban hukumar na shiyyar Legas, Mr Yomi Arowosafe, wanda ya amshi lambar yabon gwarzon ‘Pan African Telecoms Operator’ na shekara, yayin da kuma kakakin hukumar Mr Reuben Muoka ya amshi lambar yabon gwarzon jami’in sadarwa na shekara.

Dambatta ya gode wa kamfanin da suka shirya lambar yabon tare da zakule shi hadi da karrama shi. Ya nuna hakan a matsayin matakin da zai kara masa azama a fagen aiki.

Labarai Masu Nasaba

Gwamnatin Tarayya Na Yunƙurin Kawar Da Shanu Daga Titunan Abuja

Abubuwan Da Ba A Faɗa Ba Game Sulhu Da Ƴan Bindiga A Katsina

Tun da farko da yake jawabi a wajen taron, tsohon gwamnan jihar Legas, Mr Femi Pedro, ya bukaci masu ruwa da tsaki da su ke bayar da fifiko da muhimmanci ga darussan kimiyya, fasaha, injiniyanci da lissafi (STEM) tun daga matakin firemare har zuwa babban matakin karatu.

Kazalika, ya ce, lokaci ya yi da za a karfafi matasa kan hanyoyin dogaro da kai, kirkire-kirkire ta hanyar amfani da fasahar zamani, “Wasu matasa da dama suna ta korafin babu aikin yi, alhali ga hanyoyin da za a iya samun abun yi ta kimiyya ta hanyar kirkire-kirkire.

“Babu bukatar wani ya zauna babu aikin yi a duniyar yau.”

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Muhimman Abubuwan Da Takardar Karin Kudin Makarantar Sakandaren Gwamnatin Tarayya Ta Kunsa

Next Post

Kamfanin Twitter Ya Maye Gurbin Tambarin Tsuntsu Da X

Related

Gwamnatin Tarayya Na Yunƙurin Kawar Da Shanu Daga Titunan Abuja
Manyan Labarai

Gwamnatin Tarayya Na Yunƙurin Kawar Da Shanu Daga Titunan Abuja

4 minutes ago
Abubuwan Da Ba A Faɗa Ba Game Sulhu Da Ƴan Bindiga A Katsina
Manyan Labarai

Abubuwan Da Ba A Faɗa Ba Game Sulhu Da Ƴan Bindiga A Katsina

1 hour ago
NCC
Manyan Labarai

Yadda Ɗantsoho Ya Mayar Da Hankali Wajen Farafaɗo Da Martaba Da Ƙimar NPA

2 hours ago
Yadda Ciwon Hanta Ke Yaɗuwa Tsakanin Ma’aurauta
Labarai

Yadda Ciwon Hanta Ke Yaɗuwa Tsakanin Ma’aurauta

11 hours ago
Dokar Hana Ƙara Kuɗin Makaranta A Kaduna: Alheri Ce Ko Barazana Ga Makarantu Masu Zaman Kansu?
Manyan Labarai

Dokar Hana Ƙara Kuɗin Makaranta A Kaduna: Alheri Ce Ko Barazana Ga Makarantu Masu Zaman Kansu?

14 hours ago
Tinubu Ya Ziyarci Iyalan Buhari A Jihar Kaduna
Manyan Labarai

Tinubu Ya Ziyarci Iyalan Buhari A Jihar Kaduna

14 hours ago
Next Post
Kamfanin Twitter Ya Maye Gurbin Tambarin Tsuntsu Da X

Kamfanin Twitter Ya Maye Gurbin Tambarin Tsuntsu Da X

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Na Yunƙurin Kawar Da Shanu Daga Titunan Abuja

Gwamnatin Tarayya Na Yunƙurin Kawar Da Shanu Daga Titunan Abuja

September 20, 2025
Abubuwan Da Ba A Faɗa Ba Game Sulhu Da Ƴan Bindiga A Katsina

Abubuwan Da Ba A Faɗa Ba Game Sulhu Da Ƴan Bindiga A Katsina

September 20, 2025
NCC

Yadda Ɗantsoho Ya Mayar Da Hankali Wajen Farafaɗo Da Martaba Da Ƙimar NPA

September 20, 2025
Kamfanin Kasar Sin Ya Bayar Da Gudunmuwar Kayayyaki Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Sudan Ta Kudu

Kamfanin Kasar Sin Ya Bayar Da Gudunmuwar Kayayyaki Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Sudan Ta Kudu

September 19, 2025
Yadda Ciwon Hanta Ke Yaɗuwa Tsakanin Ma’aurauta

Yadda Ciwon Hanta Ke Yaɗuwa Tsakanin Ma’aurauta

September 19, 2025
An Kammala Taron Dandalin Tattauna Batun Tsaro Na Xiangshan

An Kammala Taron Dandalin Tattauna Batun Tsaro Na Xiangshan

September 19, 2025
Firaministan Sin Zai Halarci Babban Taron Mahawara Na MDD Karo Na 80

Firaministan Sin Zai Halarci Babban Taron Mahawara Na MDD Karo Na 80

September 19, 2025
Shugaba Xi ya zanta ta wayar tarho da takwaransa na Amurka

Shugaba Xi ya zanta ta wayar tarho da takwaransa na Amurka

September 19, 2025
Dokar Hana Ƙara Kuɗin Makaranta A Kaduna: Alheri Ce Ko Barazana Ga Makarantu Masu Zaman Kansu?

Dokar Hana Ƙara Kuɗin Makaranta A Kaduna: Alheri Ce Ko Barazana Ga Makarantu Masu Zaman Kansu?

September 19, 2025
Tinubu Ya Ziyarci Iyalan Buhari A Jihar Kaduna

Tinubu Ya Ziyarci Iyalan Buhari A Jihar Kaduna

September 19, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.