Biyo bayan matsanancin halin rayuwar da jama’a suka shiga sakamakon cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi, gwamna Umaru Ahmadu Fintiri, ya kafa kwamitin mutum 20, da nufin raba kayan tallafin rage radadi ga jama’ar jihar Adamawa.
Wannan na kunshe cikin wata sanarwar manema labarai da jami’in yada labaran gwamnan Humwashi Wonosikou, ya rattaba wa hannu, inda ta ce mambobin kwamitin sun fito ne daga kungiyoyi, ma’aikatu da ma daidaikun jama’a.
Sanarwar ta ce mafi yawan kayayyakin da kwamitin zai raba a matakin farko sun shafi kayan abinci.
Mambobin kwamitin da gwamna Ahmadu Umaru Fintiri zai rantsar ranar Talata, sun hada da sakataren gwamnatin jihar, Awwal Bamanga Tukur a matsayin sakatare.
Sai kuma mambobin kwamitin da suka hada sarkin Shelleng mai martaba Amna Shelleng,
Sarkin Numan mai martaba Hama Bachama, da ‘yan majalisun tarayya da ke wakiltar jihar, da kuma ‘yan majalisun dokokin jihar.
Sai kuma kwamishinan jin kai da walwalar jama’a, shugaban ma’aikatan jihar, shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi, shugaban rundunar sojin jihar da shugaban rundunar sojin sama a jihar, shugaban rundunar ‘yan sanda, daraktan DSS da kwamandan rundunar sibil defens.
Sauran su ne wakili daga kungiyar kiristoci ta kasa (CAN) reshen jihar, da wakili daga kungiyar hadin kan Musulmi, wakilin kungiyar ‘yan jaridu (NUJ), wakilin kungiyar kwadago (NLC), da TUC da NCWS da kuma wakilin ma’aikatar ba da agajin gaggawa ta jihar (ADSEMA).