Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya amince da fara aiki da motocin bas na gwamnati don tallafawa zirga-zirgar dalibai da ma’aikata a manyan makarantun gwamnati a Ilorin, babban birnin jihar, da kewaye.
Bayar da tallafin bas din ga daliban da ke babban birnin, shi ne kashi na biyu na matakan da gwamnatin jihar Kwara ta dauka na rage radadin cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi.
Tun da farko, gwamnatin ta rage kwanakin aiki na ma’aikatan gwamnati daga biyar zuwa uku a kowane mako.
Babban sakataren yada labarai na gwamnan, Rafiu Ajakaye ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a Ilorin, a ranar Lahadi.