A kokarinsa na ragewa al’umma wahalhalun da cire tallafin man fetur ya janyo, Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya kaddamar da sabon shirin tallafa wa magidanta 300,000, wanda akalla kowane gida daya akwai kimanin mutum shida (adadin mutum miliyan 1.8), mabukata a fadin jihar.
Haka kuma, Gwamna Zulum ya kaddamar da rarraba kayan abinci a ranar Alhamis din da ta gabata a Sansanin ‘Yan Gudun Hijira da ke Muna a karamar Hukumar Jere dake jihar.
Gwamnan ya bayyana cewa, jihar ta fara aikin raba tallafin tun a watan da ya gabata, domin aiwatar da manufofin shugaban kasa, bayan ayyana raba wa jama’a abinci sakamakon cire tallafin man fetur.
“A kwanan nan Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana shirin matakin gaggawa na raba wa al’ummar kasar nan kayan abinci. Wanda saboda mu tabbatar mun aiwatar da wannan kuduri na gwamnatin Tarayya wajen ganin ta saukaka wa jama’a wahalhalun da cire tallafin mai ya janyo, mun kuduri aniyar tallafa wa magidanta 300,000 da kayan abinci.” In ji Zulum.
Ya sanar da cewa jihar ta fara raba tallafin a garin Gwoza tare da wasu garuruwa uku a karamar Hukumar Kukawa wadanda suka hada da Baga, Kros Kauwa da Doron Baga.
Zulum ya ce kowane mutum daya da ya cancanta ya karbi tallafin zai samu kyautar N5,000, buhun shinkafa, buhun wake tare da karin wani kunshi (ga mata).