Wani dan kungiyar ‘yan sa-kai da ke aiki a tashar jigilar fasinjoji a Maiduguri ya cafke wata mata dauke da almajirai biyu da wata yarinya ‘yar shekara biyu da ake zargin za ta yi safararsu.
An ce matar tana hanyarta na zuwa Abuja ne a lokacin da aka kamata.
Wani direban da ke jigilar fasinjoji zuwa Abuja a tashar Maiduguri, Danjuma Mohammed, ya fada wa majiyarmu cewa, matar ta badl da sunanta da cewa Nkwenwu ta zo tashar ne dauke da yara uku maza biyu da karamar yarinya guda da ke goye a bayanta da yammacin ranar Alhamis.
Mohammed ya yi bayanin cewa a ranar Juma’a da safiya ne kuma jami’an tsaron da ke sintiri a kasuwar suka fara sanya shakku da zargin matar daga nan ne jami’an CJTF suka kamatl ta.
Jami’in CJTF mai suna Bukar ya ce binciken farko-farko da suka gudanar ya gano musu cewa yara biyun almajirai ne da suke bin kwararo-kwararo domin neman abinci, “Dan babba daga cikin almajiran shi ne Modu mai shekara 7 ya ce iyayensa ne suka kawo shi Maiduguri daga kauyensu da ke karamar hukumar Damboa, yayin da dayan yaron kuma da ya kai shekara biyar a duniya ya ce sunan mahaifiyarsa Aisha, ita kuma karamar yarinya ba ta iya magana ba.”
A lokacin da aka tuntubi kakakin ‘yansandan jihar Borno, ASP Sani Kamilu Muhammed, ya tabbatar da cafke matar da ake zargi da safarar yara, sai dai ya ce, “Amma har zuwa yanzu ban samu cikakken bayanin lamarin ba.”