Jiya Jumma’a ranar 27 ga wata, mataimakin shugaban sashen fadakar da al’umma na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda kuma shi ne shugaban babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin ko kuma CMG a takaice, Shen Haixiong, da shugaban kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa wato IOC Thomas Bach sun rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa a hedkwatar kwamitin Olympics na kasa da kasa dake birnin Lausanne na kasar Switzerland. Bisa ga yarjejeniyar, bangarorin biyu za su ci gaba da zurfafa hadin gwiwa a fannonin watsa rahotannin wasannin Olympics da inganta al’adun Olympics da dai sauransu. Bangarorin biyu sun kuma halarci bikin kaddamar tubalin tunawa da CMG a gidan adana kayan tarihi na Olympics.
A yayin shawarwarin da ya yi da Thomas Bach, Shen Haixiong ya ce, a watan Mayu na shekarar da muke ciki, karkashin amincewar shugaba Bach, an gayyaci CMG a hukumance don zama babbar hukumar watsa shirye-shirye ta gasar wasannin Olympics ta Paris na shekarar 2024, wanda ke da alhakin samar da siginar jama’a na kasa da kasa kan manyan wasanni hudu.
Kwanaki hudu da suka gabata, CMG ya kaddamar da hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tare da kwamitin shirya wasannin Olympics na Paris, inda a shekara mai zuwa kuma, zai aika da wata babbar tawagar watsa shirye-shirye zuwa birnin Paris domin gabatar da wata gasar wasannin Olympics mai ban sha’awa kuma mara misaltuwa bisa ga kwarewarsa dake kan gaba a duniya wajen watsa shirye-shiryen wasanni.
Shen Haixiong ya kara bayyana cewa, “Kwamitin Olympics na kasa da kasa ya bai wa CMG damammaki, kuma ko shakka babu za mu ba duniya mamaki!” (Mai fassara: Bilkisu Xin)