A gabannin bude dandalin taron koli, kan hadin gwiwar kasa da kasa bisa shawarar ziri daya da hanya daya karo na uku, babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG, da wasu manyan kafofin watsa labarai na kasashen Afirka, sun fitar da “shawarar aiki ta kafofin watsa labarai na kasar Sin da kasashen Afirka, kan shawarar ziri daya da hanya daya”, wadda ta samu goyon baya daga kafofin watsa labarai, da hukumomin da abin ya shafa na kasashen Afirka da yawansu ya kai 50, ciki har da kawancen kungiyoyin rediyo da talibijin ta Afirka.
Kafofin watsa labarai na Sin da Afirka, za su kara zurfafa zumuncin dake tsakaninsu ta hanyoyi daban daban. Alal misali, daukar bidiyo na hadin gwiwa, da zantawa da manyan jami’an gwamnatoci, da shirya bukukuwan nune-nunen fina-finai da wasan kwaikwayo, da kuma shirya hadaddun ayyukan watsa labarai.
Mataimakin ministan yada manufofin kasar Sin, kuma shugaban CMG Shen Haixiong, ya bayyana a cikin jawabinsa ta bidiyo cewa, bana ake cika shekaru goma, tun bayan da shugaba Xi Jinping ya gabatar da shawarar ziri daya da hanya daya, da ma gabatar da manufar sahihanci ga Afirka.
A cikin wadannan shekaru goma da suka gabata, an gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka yadda ya kamata, kuma CMG shi ma yana fata yin hadin gwiwa da kafofin watsa labarai na kasashen Afirka, wajen nuna babban sakamakon da kasar Sin da kasashen Afirka suka samu, yayin hadin gwiwarsu bisa shawarar ziri daya da hanya daya. (Mai fassara: Jamila)