A yau Alhamis 26 ga wata bisa agogon Geneva, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin ko kuma CMG a takaice, da hukumar kula da ikon mallakar fasaha ta duniya wato WIPO, sun rattaba hannu kan takardar neman yin hadin gwiwa a birnin Geneva na kasar Switzerland, inda bangarorin biyu za su yi hadin gwiwa wajen karfafa ba da kariya da fadakar da ikon mallakar fasaha, da gudanar da ayyukan musaya tsakanin kasa da kasa da dai sauransu.
Mataimakin shugaban sashin fadakar da al’umma na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda kuma shi ne shugaban CMG Shen Haixiong da darakta janar na hukumar WIPO Daren Tang ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar a madadin bangarorin biyu. Jakada Chen Xu, zaunannen wakilin kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva da sauran kungiyoyin kasa da kasa dake kasar Switzerland, ya halarci bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar. (Mai fassara: Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp