A ranar 25 ga watan Yuli, agogon kasar Faransa, an fitar da “Rahoton Sabunta Fasaha da Raya Bangaren Watsa Labarai Kai Tsaye na Wasannin Olympics na CMG” cikin harsunan Sinanci da Ingilishi da Faransanci da sauran nau’ikan harsuna da dama a birnin Paris. Daraktan CMG Shen Haixiong ya shaida yadda aka fitar da rahoton a dakin watsa shiri da ke cikin cibiyar yada labarai ta kasa da kasa ta wasannin Olympics na birnin Paris na kasar Faransa.
Wannan rahoton da Cibiyar Bincike ta CMG ta wallafa ya ba da cikakken bayani game da tsarin ci gaba na CMG a fasahohin 5G, da AI, da kayayyakin aiki na musamman, da sauran fannoni, kuma an nuna dimbin damammakin hadin kan fasahar watsa labaru da wasannin motsa jiki a nan gaba.
- Sin Tana Dora Muhimmanci Kan Dangantakar Abokantaka Ta Gargajiya Da Rwanda
- Kasar Sin Tana Da Tashoshin 5G Miliyan 3.92
Sannan kafar CMG ta kaddamar da studiyonsa na watsa shirye-shirye kai tsaye a gaban hasumiyan Eiffel a hukumance. Shugaban CMG Shen Haixiong ya duba yadda aiki ya kankama a wurin.
Studiyon ya kammala gwaje-gwajen kayayyakin aiki, kuma zai fara watsa shirye-shirye a yau. Ta hanyar sarrafa fayafayen bidiyoyi, hotuna da sauti na ainihi da fasaha ta musamman, CMG zai samar da yanayi mai daukar hankali wajen gabatar da ingataccen aikin watsa shirye-shiryen gasar Olympics, tare da nuna gwanintar watsa shirye-shire ga masu kallo (Masu fassarawa: Bello Wang, Yahaya)