A yau ne, babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG ya gudanar da rahaza karo na 1 na shagalin murnar sabuwar shekarar 2025 bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, don gwada shirye-shiryen shagalin da yin amfani da sabbin fasahohin zamani tare.
Wannan ne karo na farko da aka gudanar da shagalin bayan da aka nada bikin Bazara na al’ummar Sinawa a matsayin abin gado wanda ba na kaya ba, bisa taken “Fatan alheri da samun ci gaba” da yanayin jin dadi, an gabatar da shirye-shiryen wake-wake da raye-raye, da wakokin gargajiya, da wasan kwaikwayo mai dariya da sauransu don maraba da bikin Bazara. Kana an shigar da abubuwan dake shafar al’adun gargajiya na kasar Sin don nuna wa masu kallo a ciki da waje, shagalin al’adu mai nishadantarwa. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp