Kwanan baya shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gudanar da ziyarar aikinsa a karon farko a kasar Hungary, bisa gayyatar da takwaransa Sulyok Tamas, da firaministan kasar Orbán Viktor suka yi masa.
Shirin zantawa da manyan shugabanni na CMG ya tattauna da firaministan kasar a birnin Budapest, fadar mulkin kasar.
Xi Jinping ya gudanar da ziyarar aiki a Hungary, bayan ya kammala ziyara a kasashen Faransa da Serbia. Yayin da aka tabo batun ma’anar ziyarar Xi Jinping a wannan karo, ga ingiza huldar Sin da Hungary, da ma Sin da Turai har ma a dukkanin fadin duniya, Orbán Viktor ya ce, ziyarar Xi Jinping a wannan karo ta ba da sako mai yakini, kuma ta bayyana matsayin da Sin ke dauka na bude kofa, da niyyar inganta hadin kanta da kasashen Turai. Don haka ziyarar ta kyautata halin da ake ciki, ta kuma bayyanawa shugabannin kasashen Turai cewa, Sin ta zo da zarafi, kuma kamata ya yi a nacewa hanyar da ta dace wato ta kara hadin kai.
Kaza lika, game da ikirarin da wasu kasashen Turai suke yi cewa wai za su yi bincike kan kamfanonin Sin masu samar da motoci dake amfani da makamashi maras gurbata muhalli, mista Orbán Viktor ya ce, matakin ba ma kawai zai yi mummunan tasiri ne ga wasu kasashe ba, har ma zai illata moriyar EU baki daya. Don haka dole ne a dauki kasar Sin a matsayin wani zarafi mai kyau, maimakon barazana ko kalubale.
Daga nan sai ya nanata cewa, idan har ana son zama kan gaba a duniya, dole ne a rike karfin takara mai inganci, ta amfani da karfin kashin kai, ba wai dakile bunkasuwar wasu ba. (Amina Xu)