A yau ne, babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG ya gabatar da tambarin musamman da kayan murnar bikin bazara na kasar Sin na shekarar 2023 mai alamar zomo, mai suna “Tu Yuan Yuan” a hukumance.
Za a yi amfani da kayayyakin ne a gun bikin murnar ranar bikin bazara mai taken “kara jin dadin zaman rayuwa a kasar Sin a sabon zamani”.
Bayan hakan, an shaida cewa an kusantar da lokacin ranar bikin murnar bikin bazara na CMG na shekarar 2023.
Kuma kayayyakin fatan alheri na Tu Yuan Yuan mai salon gargajiya tare da salon zamani zai yi wa masu kallo fatan alheri a ranar bikin, kafin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp